ABNA24 : Wannan furucin na Saudiyya na zuwa ne kwanaki kadan bayan kulla alakar diflomatsiyya ba zata tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Israi’lar.
Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Berlin na kasar Jamus, ministan harkokin wajen Saudiyya, Fayçal Ben Farhane, ya ce, dole ne a samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da kuma Falasdinu, bisa tanadin dokokin kasa da kasa da aka amince dasu.
Kuma idan hakan ta tabbata to akwai yiwuwar mu kulla alaka da Isra’ila, inji shi.
Kallaman na Saudiyya dai sun shan bambam da na kawarta Hadaddiyar daular Larabawa wacce ta sanar da kulla alaka da Isra’ila a kwanakin baya.
Saidai masana na ganin ko da hukumance babu wata alaka tsakanin Saudiyya da Israila, amma an jima ana tattaunawa ta bayan fage tsakanin bangarorin biyu aminnan Amurka na kud-da-kud, kuma abokan gaban Iran.
A halin da ake ciki dai kasashen Bahrain da Oman ne ake hasashen cewa suna shirin kulla alaka da Isra’ila, wanda zabi ne mai wuya ya rage masu na ko su bi sahun Saudiyya ko Hadaddiyar Daular Larabawar.
342/